Isa ga babban shafi

Ba za mu biya kudin fansa don karbo daliban Kuriga ba -Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinnubu ya umurci jami’an tsaron kasar da kada su biya ko da sisin kwabo a maytsayin kudin fansar daliban wata makaranta su kusan dari 3 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. 8/05/23
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. 8/05/23 AP - Ben Curtis
Talla

A maimakon haka,Tinubu ya umurci hukumomin tsaron su tabbbatar da ceto wadannan dalibai ba tare da sun biya masu garkuwa da su ba, kamar yadda ministan yada labaran kasar, Mohammed Idris ya shaida wa manema labarai.

A makon da ya gabata ne ‘yan bindiga suka yi awon gaba da dalibai kimanin 286 daga makarantar firamare na garin Kuriga da ke jihar Kaduna a Najeriya, inda suka nemi a biya su kudin fansa da ya kai naira biliyan guda, kwatanntacin dalar Amurka dubu dari 6 da dari 4 da 32.

Jubril Aminu Kuriga, wanda shugaba ne ana matasa a garin, kuma kakakin iyalan da aka yi garkuwada ‘yayansu ya bayyana cewa masu garkuwar sun kira shi ta wayar hannu a ranar Talata, inda suka bukaci wadannan makudan kudade.

Shi ma Idris Ibrahim, wanda zababben kansila ne na mazabar kuriga ya tabbatar da wannan bukata ta masu garkuwa da daliban.

Wannan ne karo na farko da aka yi satar dalibai masu yawa a Najeriya tun bayan wadanda aka yi a shekarar 2021.

Wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a shekaru 3 da suka wuce, a sake su ne bayan da aka biya kudin fansa.

Wata doka da majalisar dokoki ta amince da ita a shekarar 2022 ta haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane a  Najeriya.

Ta’azzarar satar mutane don karbar kudin fansa a Najeriya ta zame wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu karfen kafa, duba da cewa ya sha alwashin kawo karshen matsalar tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.