Isa ga babban shafi

Shell zai bai wa kamfanin takin Dangote kubik miliyan 100 na gas kowacce rana

Najeriya – Katafaren kamfanin hakar man Shell ya bayyana shirin bai wa kamfanin sarrafa takin Dangote dake Lagos iskar gas da yawan sa ya kai kubik miliyan 100 kowacce rana domin amfani da shi a masana'antarsa.

Alhaji Aliko Dangote.
Alhaji Aliko Dangote. © Twitter/Dangote Group
Talla

Kamfanin yace ya yanke hukuncin daukar wannan mataki ne na zuba jari a kamfanin tare da abokan aikin sa irin su NNPC da TotalEnergies da EP da kuma Agip.

Sanarwar tace yarjejeniyar da bangarorin suka cimma zata kwashe shekaru 10 ana gudanar da ita.

Matatar Dangote dake Lagos
Matatar Dangote dake Lagos REUTERS - TEMILADE ADELAJA

Mai magana da yawun kamfanin Shell Abimbola Essien-Nelson yace shugaban kamfanin Shell Osagie Okunbor ya bayyana cewar wannan yarjejeniyar zuba jarin wata gagarumar ci gaba ne mai matukar tasiri ga tattalin arzikin Najeriya.

Kamfanin Dangote na samar da kashi 65 na takin zamani samfurin yuriya da manoma ke bukata a nahiyar Afirka daga masana'antar sa dake unguwar Lekki a Lagos.

Shugaban kamfanin Aliko Dangote yace yace samar da gas din zai taimakawa Najeriya wajen samun karin kudaden waje da kuma ci gaba da zaman kasar a matsayin ta farko cikin jerin masu samar da taki a Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.