Isa ga babban shafi

Sojojin Najeriya sun kashe Kachalla da wasu kwamandodin 'yan bindiga a Neja

Najeriya – Rundunar tsaron sojin Najeriya ta sanar da kashe daya daga cikin manyan kwamandojin ‘yan bindigar da suka hana jama’a zaman lafiya a jihar Zamfara da Neja, wanda ake kira Kachalla tare da wasu kwamandodi guda 3 sakamakon hare haren da aka kai musu.

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa © Sawaba Radio
Talla

Daraktan yada labaran dake sanya ido a kan ayyukan da bangarorin sojin kasar keyi, Manjo Janar Edward Buba ya sanar da wannan nasarar da suka samu a wata sanarwar da ya rabawa manema labarai yau asabar.

Buba ya bayyana sunayen kwamandodin da suka kashe da suka hada da Machika da Haro da Dan Muhammadu da kuma Ali Alhaji Alheri da aka fi sani da suna Kachalla Ali Kawaje.

Daraktan ya bayyana Machika a matsayin masanin hada bama bamai kana kuma kani ga fitaccen ‘dan bindiga Dogo Gide, yayin da ya kuma ce Haro da Dan Muhammadu sun yi fice wajen garkuwa da mutane da kuma kai hari a kan jama’a.

Buba yace wasu hare haren hadin gwuiwa da sojojin sama da kasa suka kai a ranar 11 ga watan nan ya ritsa da kwamandodin, cikinsu harda Kachalla Kawaje da ya jagoranci sace daliban jami’ar gwamnatin tarayya ta Gusau, wanda yace an hallaka shi ne a karamar hukumar Munya dake jihar Neja tare da wasu mukarrabansa.

Daraktan yace wadannan ayyukan da sojojin suka yi, sun taimaka wajen kashe ‘yan ta’adda 38 tare da kama 159.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.