Isa ga babban shafi
HARIN KADUNA

Najeriya: MDD ta bukaci a yi bincike kan harin da aka kai wa masu bikin Maulidi

Majalisar dinkin duniya, ta bukaci a gudanar da sahihin bincike kan musabbabin kisan masu Maulidi akalla 85 a wani kauye da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Wakilan rundunar sojin Najeriya kenan da suka kai ziyara kauyen da ibtila'in ya faru a jihar Kaduna.
Wakilan rundunar sojin Najeriya kenan da suka kai ziyara kauyen da ibtila'in ya faru a jihar Kaduna. © Premiumtimes
Talla

Ofishin hukumar kare hakkin dan adam na Majalisar, ya lura da cewa, hukumomin kasar sun bayyana hatsarin a matsayin rashin sani, amma dai ya bukaci a dauki matakan kariya domin kaucewa faruwar hakan a nan gaba.

Wata sanarwa da kakakin ofishin hukumar, Seif Magango ya fitar, ta ce ya kamata Najeriya ta gudanar da sauye-sauye kan yadda sojoji ke gudanar da aikinsu, domin tabbatar da cewa hakan be sake faruwa akan fararen hula ba.

Ofishin hukumar ya bukaci gwamnatin Najeriya, da ta gudanar da cikakken bincike, tare da daukar tsauraran matakai kan wadanda aka samu suna da laifi.

Tuni shugaban Najeriyar, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin harin da ya auku a kauyen Tudun Biri, da ke arewa maso yammcin jihar Kaduna, lokacin da mazauna yankin ke tsaka da gudanar da bikin Maulidi.

Da dama daga cikin mutanen da lamarin ya rutsa da su, mata ne da kananan yara da kuma masu dogon shekaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.