Isa ga babban shafi
labarin aminiya

An harbi’ masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Kaduna

’Yan sanda a Jihar Kaduna sun tarwatsa ’yan kungiyar ’yan uwa Musulmi ta Najeriya (IMN) ta mabiya Shi’a da ke zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa.

Jami'an tsaron Najeriya.
Jami'an tsaron Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Masu zanga-zangar dai na goyon bayan Falasdinawan ne wadanda yanzu haka ƙasar Isra’ila ke yi wa luguden wuta a Zirin Gaza.

’Yan Shi’ar dai sun fara zanga-zangar ne dai daga sakatariyar Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) sannan suka bi titin Muhammadu Buhari, zuwa ofishin Hukumar Kare Hakkin Ɗan Adam (NHRC), inda suka mika takardar kokensu.

Sai dai ’yan mintuna bayan fara zanga-zangar, sai ’yan sanda suka fesa musu barkonon tsohuwa sannan suka yi harbi a sama domin tarwatsa su.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce sakamakon harbin, mutum biyu sun rasa ransu.

Aliyu Umar Tirmizi, wanda ya yi magana a madadin masu zanga-zangar, ya ce, “Tsawon shekara 75 ke nan Isra’ila na aiwatar da kisan kiyashi da kisan kare-dangi da wariyar launin fata a kan fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba, cikinsu har da maza, mata da ma kananan yara.

“Sun kashe dubban kananan yara da tsofaffi sannan sun lalata wuraren ibada da na ibadar mutanen da ba ruwansu.

“Waɗannan Yahudawan na Isra’ila sun keta alfarmar masallacin birnin Kudus, sun hana mutane zuwa ciki domin yin ibada,” in ji Timizi.

Tun bayan harin rokoki da kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta kaddamar a kan Isra’ila, kasar ta ke kai hare-haren ramuwar gayya, inda zuwa yanzu ta kashe sama da mutum 12,000 a Zirin Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.