Isa ga babban shafi

Hadaddiyar Daular Larabawa ta janye haramcin takardar biza ga 'yan Najeriya

Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta janye matakin da ta dauka na haramtawa ‘yan Najeriya takardar izinin shiga cikinta, yayin da kuma kamfanin jiragen samanta na Emirates zai ci gaba da jigilar sufuri zuwa Najeriyar.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Mohamed bin Zayed Al Nahyan a birnin Abu Dhabi.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Mohamed bin Zayed Al Nahyan a birnin Abu Dhabi. © Twitter/@NGRPresident
Talla

Wannan mataki ya biyo bayan ganawar da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi da takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa Mohamed bin Zayed Al Nahyan a Abu Dhabi.

Domin jin karin bayan akan matakin ne ya sa muka tuntubi Yusuf Tugga Ministan harkokin wajen Najeriya

01:00

Yusuf Tugga Ministan harkokin wajen Najeriya

A shekarar da ta gabata gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta dakatar da bayar da takardar biza ga 'yan Najeriya saboda makalewar da kudaden Emirates yayi a kasar, lamarin da ya sa kamfanin jiragen saman na Emirates da takwaransa na Etihad suka dakatar da zirga-zirgar jiragensu zuwa Najeriyar.

A watannin baya bayan nan Najeriya ta fuskanci kalubalen karancin dala, lamarin da ya shafi kamfanonin jiragen sama na kasashen waje, wadanda ke sayar da tikitinsu da kudin kasar na Naira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.