Isa ga babban shafi

Gwamnan Neja ya nada mata 131 a matsayin masu taimaka masa

Gwamnan Jihar Neja dake Najeriya Mohammed Umaru Bago ya nada mata 131 a matsayin wadanda zasu taimaka masa gudanar da ayyukan sa a jihar. 

Mutanen Ogoni a yankin Neja Delta mai arzikin fetir a Najeriya
Mutanen Ogoni a yankin Neja Delta mai arzikin fetir a Najeriya AFP PHOTO
Talla

Mai magana da yawun sa Bologi Ibrahim yace, daga cikin matan 131 da aka nada, 41 zasu zama masa kodineta a yankunan jihar, yayin da 90 kuma za su rike mukamin manyan masu taimaka masa da ake kira da turanci SSA. 

Tasiwrar Najeriya da ke nuna jihar Neja.
Tasiwrar Najeriya da ke nuna jihar Neja. © Wikimedia Commons

Gwamnan ya bukaci wadanda aka nada da su jajirce wajen bada gudumawa ta hanyar da gwamnatin sa zata samu nasarar sauke nauyin da aka dora mata. 

Wasu daga cikin mata masu neman hakokkinsu
Wasu daga cikin mata masu neman hakokkinsu RFI / Yaya Boudani

Bago yace nada wadannan tarin mata na daga cikin alkawarin da yayi lokacin yakin neman zabe na bas u damar taka rawa a cikin gwamnatin sa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.