Ginin babban Masallacin Zazzau ya rufta kan masallata
Akalla Masallata hudu sun rasa rayukansu, yayin da wasu jikkata bayan ginin babban Masallacin kofar fadar sarkin Zazzau ya rufta musu.
Wallafawa ranar:
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa, lamarin ya rutsa da Masallatan ne a daidai lokacin da suke gudanar da sallar la'asar da misalin karfe hudu na yamma.
Sarkin ya bayyana cewa, tun jiya aka lura da tsagewar bangon masallacin, inda kuma ake shirin kawo kwararrun injiniyoyi domin gyaran garun, yayin da wannan tsautsayi ya faru a Juma'ar nan gabanin aiwatar da gyaran.
Tuni Sarkin na Zazzau ya mika sakon ta'aziya ga iyalan mamatan, sannan ya bada umarnin ci gaba da gudanar da salla a wajen harabar Masallacin kafin kammala gyara.
Za a gudanar da sallar jana'izar mutanen da suka rasun da misalin karfe 8 da rabi na dare a fadar sarkin na zazzau da ke Kaduna a Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu