Isa ga babban shafi

Najeriya: El-Rufai da Wike na daga cikin tawagar ministocin Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya mika sunayen wasu mutane 28 a matsayin ministocin sa. Jerin sunayen harda tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da kuma tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike. Sunayen na kunshe ne a wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisar a wannan Alhamis.

Barr. Hannatu Musawa daya daga cikin wadanda shugaban Najeriya Bola Tinubu ya zaba amtsayin ministocinsa.
Barr. Hannatu Musawa daya daga cikin wadanda shugaban Najeriya Bola Tinubu ya zaba amtsayin ministocinsa. © Barr. Hannatu Musawa
Talla

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ne ya mikawa majalisar dattijai jerin sunayen ministocin.

Gabatar da sunayen ministocin ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin kasar na kwanaki 60 daga ranar da aka rantsar da sabon shugaban kasa dole ya nada ministoci.

A cikin jerin sunayen ministocin da shugaban majalisar dattawan ya karanta, sun hada da tsofaffin gwamnoni, masana tattalin arziki, masana kiwon lafiya, lauyoyi da abokan Mista Tinubu kai tsaye.

Baya ga Malam El-Rufai da Wike, sauran sunayen sun hada da tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Oyo, Adebayo Adelabu, babban lauya Lateef Fagbemi, masanin tattalin arziki Olawale Edun da kuma mai magana da yawun shugaban kasa Dele Alake, da kuma Barr. Hannatu Musawa wanda ya nada amatsayin mashawarciya ta musamman.

Shugaba Tinubu ya bukaci majalisar dattawa da ta tantance tare da tabbatar da sunayen ministocin.

Ga jerin sunayen kamar yadda aka karanta:

Abubakar Momoh

Amb. Yusuf Maitama Tugga

Arc. Ahmed Dangiwa

Barr. Hannatu Musawa

Uche Nnsaji

Peter Edu

Sen. David Umahi

Nyesom Wike

Badaru Abubakar

Nasiru El-Rufai

Nkiru Onyejiocha

Olubunmi Ojo

Stella Okotete

Ujo Kennedy Ohaneye

Bello Mohammed

Dele Alake

Lateef Fagbemi

Mohammed Idris

Waheed Adelapo

Emman Suleiman Ibrahim

Farfesa Ali Pate

Farfesa Jeseph Amfani

Abubakar Kyari

John Eno

Sani Abubakar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.