Isa ga babban shafi

'Yan sandan Najeriya sun bindige mahaukaci bayan ya fille kan wani dattijo

Wani magidanci mai shekaru 32, David Shodola, wanda ake zargin yana da tabin hankali, ya jefa garin Ipara da ke karamar hukumar Remo-Arewa ta jihar Ogun cikin rudani a ranar Jumma’a, bayan da ya fille kan wani dattijo mai shekaru 84, Alfred Opadipe. Sai dai ‘yan sandan a jihar sun harbe mahaukacin bayan da aka ce ya bijirewa kama shi.

Alamar 'Yan sandan Najeriya
Alamar 'Yan sandan Najeriya Nigeria Police Force
Talla

Wani faifan bidiyo mai tsawon minti tara da dakika takwas, da aka yada a kafofin sada zumunta na intanet a ranar Juma’a, ya nuna gawar mahaukacin a kasa sannan nesa da shi kadan ana ganin wani kai da ake zargin na dattijon da ya fille ne.

Wani ganau, wanda ya yi magana a cikin faifan faifan, ya bayyana cewa mahaukacin ne ya kashe dattijon wajen fille masa kai.

Jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Omotola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta ranar Juma’a.

Bukatar dauki

Odutola ta ce rundunar ta samu kiran gaggawa daga wani mazaunin unguwar da lamarin ya faru wanda ya basu labari kan lamarin, yayin da aka tura ‘yan sanda karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda na Isara, CSP Bankole Eluyeru a wurin.

Ta ce, “Rundunar ‘yan sandan shiyya ta Isara, CSP Bankole Eluyeru, ya yi yunkurin cafke wanda ake zargin, amma ya yi amfani da adduna wajen kare kansa wajen tinkarar jami’an tsaro da sauran mutane, abin da ya sa aka bindigeshi har lahira.

Tabin hankali

Sai dai jami’ar ta ce, babu alaman wanda ake zargin yana da tabin hankali daga bayanan sirrin da ‘yan sandan suka tattara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.