Isa ga babban shafi

Sojojin Najeriya sun kubutar da mutane 24 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

Dakarun rundunar Operation Hadarin Daji sun samu nasarar ceto mutane 24 da aka yi garkuwa da su a Kabugu Lamba da ke karamar hukumar Maru ta jahar Zamfara.

Sojojin Najeriya a fagen daga dake arewacin kasar
Sojojin Najeriya a fagen daga dake arewacin kasar AFP
Talla

Wata majiya ta shaidawa gidan talabijin na Channels cewa, sojojin sun samu wani rahotannin sirri ne kan maboyar ‘yan ta’addan da ke dajin, inda aka tsare da wadanda akayi garkuwa da su.

Haka nan, wata majiyar soji ta shaida wa wakilin gidan talabijin din cewa, bayan samun labarin ne sojojin suka dauki matakan gaggawa wajen kai hari wurin, inda aka yi musayar wuta tsakanin ‘yan bindigar da dakarun sojojin na tsawon lokaci, wanda ya sa ‘yan bindigar gudu suka bar wadanda suka yi garkuwa da su a cikin wasu gine-gine.

A arangamar, sojojin sun yi nasarar kubutar da mutane 24 da aka yi garkuwa da su tare da kashe wasu ‘yan bindiga hudu, ya yin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Daga cikin wadanda aka kubutar sun hada da mata tara da maza 14 sai kuma wani karamin yaro daya kuma tuni aka mika su ga hukumomin da suka dace domin sada su da iyalansu.

A yayin gudanar da bincike, wadanda aka yi garkuwa da su, sun bayyana cewa wasu daga cikin su sun shafe kwanaki 21 zuwa 53, a hannun masu garkuwa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.