Isa ga babban shafi

An cika shekaru 9 da sace daliban makarantar Chibok

Yau ake cika shekaru 9 da mayakan Boko Haram suka sace ‘yan mata daliban makarantar sakandaren Chibok a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya a ranar 14 ga watan Afrilu na shekarar 2014.

Wasu daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok da aka ceto daga hannun Boko Haram a shekarar 2016, yayin da suke ganawa da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, a Abuja.
Wasu daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok da aka ceto daga hannun Boko Haram a shekarar 2016, yayin da suke ganawa da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, a Abuja. AP - Sunday Aghaeze
Talla

A waccan lokacin dai dalibai 276 mayakan na Boko Haram suka sace, kuma bayan shafe kusan shekaru 10, har yanzu akwai ragowar daliban mata 98 da suke cigaba da zama a hannun ‘yan ta’addan.

Lamarin dai ya fusata kasashe da manyan hukumomi na kasa da kasa, wadanda ke ci gaba da matsa wa gwamnatin Najeriya kan ta gaggauta ceto ragowar daliban.

Bayanai dai na nuni da cewar tuni aka tilasta aurar da wasu daga cikin daliban na Chibok a tsakanin ‘ya’yan kungiyar ta Boko Haram, yayin da kuma wasunsu suka zabi cigaba da zama a hannunsu, maimakon komawa ga iyayensu, lamarin da ake alakantawa da cusa musu ra’ayin zabin hakan da suka yi.

Kididdiga ta nuna cewar kawo yanzu  daliban sakandaren na Chibok 178 ne suka tsira daga  hannun kungiyar Boko Haram, cikinsu har da 25 da suka sulale daga hannun mayakan bayan sace su da suka yi daga makarantarsu a 2014.

Akasarin daliban da suka kubutan dai sun yi fama da matsaloli na firgici sakamakon fyade ko  auren tilas da aka yi  musu, abinda ya sa wasu komawa ga iyayensu ko dai dauke da juna biyu, ko kuma tare da yarann da suka haifawa mayakan Boko Haram.

Sai dai wani abin kwarin gwiwa da aka gani shi ne yadda akalla 80 zuwa 84 daga cikin daliban na Chibok da suka shiga tashin hankalin suka samu nasarar cigaba da  karatu zuwa matakin jami’a, kuma mafi rinjaye daga cikinsu sun samu nasara a karatun nasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.