Halin da mabarata ke ciki lokacin azumin Ramadan a Najeriya
Masu ruwa da tsaki na ci gaba da kiraye-kirayen ya kamata a kawo karshen barace-barace a Najeriya, ta hanyar samar da wani shiri da zai rika wayar da kan mutane.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kunna - 03:11
Masu karamin karfi da dama ne kan fita neman na abinci, musamman idan aka ce lokaci ne na azumin watan Ramadan, inda za ka iske suna ta fafutukar neman abin da za su yi buda baki da shi.
A wasu yankunan, masu hannu da shuni kan yi kokari wajen bayar da sadaka ga masu karamin karfi a cikin watan mai alfarma.
Wakilin RFI, Faruk Yabo, ya duba halin da masu karamin karfi ke ciki a wannan lokaci, inda ya gano yadda yara da dama suka tsunduma neman na abinci ta hanyar bara.
Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken rahotonsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu