Isa ga babban shafi

An samu karin mutum 142 da zazzabin Lassa ya kashe a Najeriya - NCDC

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya, ta ce cikin kasa da watanni uku, an samu rahoton mutane 784 da suka kamu da zazzabin Lassa, inda mutum 142 suka mutu a jihohin kasar 23.

Wani jami'in lafiya sanye da kayan kariya don zubar da sharar magunguna da ake amfani da su don kula da masu cutar zazzabin Lassa.
Wani jami'in lafiya sanye da kayan kariya don zubar da sharar magunguna da ake amfani da su don kula da masu cutar zazzabin Lassa. AFP/File
Talla

NCDC a shafinta na yanar gizo, ta ce an samu rahoton mutanen da suka kamu da cutar ne, daga watan Janairun 2023 zuwa yanzu.

Hukumar ta ce, an samu rahoton bullar cutar ne a jihohin Edo, Ondo, Ebonyi, Bauchi, Taraba, Benue, Rivers, Plateau, da kuma Nasarawa.

NCDC ta ce a jimilla daga mako na 1 zuwa mako na 11, a 2023, an samu rahoton mutuwar mutane 142 daidai da kashi 18.1 cikin 100 wanda ya yi kasa da kashi 18.7 na shekarar 2022.

A cewar hukumar, daga cikin jimillar 2023 da aka samu, jihohi 23 sun sami rahoton akalla guda daya da aka tabbatar sun harbu da zazzabin Lassa a kananan hukumomi 97.

Hukumar kula da lafiyar al’umma ta ce kashi 71 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar zazzabin Lassa sun fito ne daga Ondo, Edo da Bauchi yayin da kashi 29 cikin 100 sun fito daga sauran jihohi shida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.