Isa ga babban shafi

IPOB ta shiga sahun kungiyoyin ta'addanci mafiya hatsari a duniya

Alkaluman da cibiyar nazari kan zaman lafiya da tattalin arziki ta Duniya ta tattara ya nuna raguwar tasirin ayyukan ta’addanci a Najeriya, duk da cewa rahoton cibiyar na GTI ya sanya kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafra a sahun manyan kungiyoyin ta’addanci 20 mafiya hadari a Duniya.

Jagoran kungiyar Biafra Nnamdi Kanu.
Jagoran kungiyar Biafra Nnamdi Kanu. AFP - STEFAN HEUNIS
Talla

Cikin rahoton na GTI da cibiyar nazari kan zaman lafiya da tattalin arziki ta duniya mai shalkwata a Australia ta fitar a talatar makon nan ya bayyana IPOB a matsayin ta 10 a sahun kungiyoyin ta’addanci mafiya hadari a duniya, bayan kai hare-hare 40 tare da kashe mutane 57 cikin 2022 wanda ke nuna karuwar ta’addancin kungiyar idan an kwatanta da ta’asar da ta aikata a 2021 inda ta kai hare-hare 26 tare da kashe mutane 34.

Rahoton na GTI ko kuma Global Terrorism Index da ke sanya idanu kan karuwa ko raguwar barazanar ta’addanci a kasashe ta ce bayan ISWAP babbar barazanar Najeriyar a yanzu ita ce kungiyar ta IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra wadda tuni gwamnatin kasar ta ayyana a matsayin kungiyar ta’addanci tun a shekarar 2017.

Rahoton ya ce Najeriya na sahun kasashen da ke samun raguwar ayyukan ta’addanci inda yanzu haka ta zama kasa ta 8 a sahun ‘yan goman farko mafiya fama da hare-haren ta’addanci daga mataki na 6 da ta ke a 2021.

Najeriyar wadda ta shafe shekaru fiye da 3 a matsayin ta 3 wajen yawaitar hare-haren ta’addanci gabanin sakkowa zuwa 6 a bara waccan, rahoton ya ce a baya-bayan nan maimakon ta’addancin da ya ta’azzara a baya, yanzu arangama tsakanin batagari da jami’na tsaro shi ke taimakawa wajen haddasa asarar rayuka a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.