Isa ga babban shafi

NDLEA ta cafke mutum 12 da ake zargi da safarar wiwi zuwa Najeriya

Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun kwayoyi ta Najeriya ta cafke tabar wiwi da aka yi safararta zuwa kasar ta ruwa da kuma sama.

Shugaban hukumar NDLEA na Najeriya kenan Janar Buba Marwa mai ritaya
Shugaban hukumar NDLEA na Najeriya kenan Janar Buba Marwa mai ritaya © daily trust
Talla

Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce jami’anta sun kama tabar ne a wiwin ne a tashar jiragen ruwa ta Apapa da kuma filin jirgin sama na Murtala Mohammed dukkaninsu a birnin Legas.

Sanarwar da NDLEA ta wallafa a shafinta na twitter, ta tabbatar da cewa an shigo da tabar wiwin zuwa kasar ne daga Canada da kuma Afirka ta Kudu.

NDLEA ta ce bisa binciken da ta yi an gano cewa an shigar da wiwin ne domin hada-hadarta a lokacin bukukuwan Kirismeti da na sabuwar shekara.

Yanzu haka dai NDLEA ta cean kama mutane 12 daga cikin wandanda ake zargi da alaka wajen shigar da wiwin ta ruwa da kuma ta sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.