Isa ga babban shafi

Mun cafke masu safarar kwaya sama da 23,000 a Najeriya - NDLEA

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta ce ta kama fiye da kwayoyi na naira 100 na maganin Opioid, Tramadol wanda ka iya yin illa ga matasa.

Yadda jami'an hukumar NDLEA suka kona kusan tan biyu na hodar ibilis da aka kame a jihar Legas
Yadda jami'an hukumar NDLEA suka kona kusan tan biyu na hodar ibilis da aka kame a jihar Legas © rfi
Talla

Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa Mai Ritaya ne, ya bayyana haka ne a Abuja yayin bikin bayar da lambar yabo ga sabbin hafsoshin da suka samu karin girma.

“Hukumar ta NDLEA, ta kama masu safarar miyagun kwayoyi 23,907, kuma an kama fiye da ton 5,500 ko kuma kilogiram 5.5 na haramtattun kwayoyi, wadanda tare da kudaden da aka kama sun haura  naira biliyan 450.

“Mun kai kololuwa a yakin da muke yi da masu noman wiwi ta hanyar lalata gonakin wiwi mai fadin hekta 772.5. A cikin wadannan watanni 22, muna da bayanai na masu laifi 3,434.

Hakazalika, mun sami ci gaba mai kyau a kokarinmu na rage ta’ammali da miyagun kwayoyi, inda adadin wadanda muka bawa kulawa ta musamman domin daina ta’ammali da miyagun kwayoyi adadinsu ya kai 16,114,” in ji Marwa.

Shugaban hukumar y ace, alkaluman kididdiga da aka tattara an yi la’akari ne da irin  tasirin da miyagun kwayoyi suka yi ga rayuwar mutane, musamman matasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.