Isa ga babban shafi

Sojoji sun kashe kwamandan 'yan bindiga a Kaduna

Jami’an tsaron Najeriya sun bindige wani kasurgumin kwamandan ‘yan bindigar da suka addabi jihar Kaduna mai suna Dogo Maikasuwa.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

 

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta ce, Dogo Maikasuwa da ake yi wa lakabi da Dogo Maimillion, shi ne ya jagoranci wasu jerin hare-hare da sace-sacen mutane akan hanyar Kaduna zuwa Kachia da kuma wasu wurare a kananan hukumomin Chikun da Kajuru.

Sanarwar ta ce, wannan dan ta’addar na yawan sanya kakin sojoji, sannan yana rike bindiga kirar AK47 kuma a cikin kakin na sojoji ne aka kasha shi.

Tuni gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai ya jinjina wa sojojin da suka yi arangama tare da aika wannan dan bindigar lahira.

Jihar Kaduna na cikin jihohjin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar ‘yan bindiga masu satar mutane suna karbar kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.