Isa ga babban shafi

NNPC da kamfanin Korea ta kudu sun kulla yarjejeniyar gyaran matatar man Kaduna

Kamfanin man Najeriya na NNPC ya rattaba hannu a kwangilar gyara matatar man Kaduna tare da kamfanin Daewoo na kasar Korea ta kudu.

Shugaban Kamfanin Mai na NNPC da ke Najeriya, Mele Kyari
Shugaban Kamfanin Mai na NNPC da ke Najeriya, Mele Kyari © Guardian
Talla

Tuni kamfanin na Daewoo ya fara aikin gyara matatar Warri wadda ake saran ta fara aiki a tsakiyar shekara mai zuwa.

Ana saran Najeriya ta kashe dala biliyan guda da rabi wajen wannan gagarumin aikin wanda ya hada da na matatar Warri da kuma Kaduna.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da karamin ministan mai Dipreye Silva da shugaban kamfanin man NNPC Mele Kyari suka jagoranci taron sanya hannu akan kwangilar gyara matatar.

Najeriya wadda ke ta daya wajen arzikin man fetur a nahiyar Afirka kuma wakiliya a kungiyar OPEC ta gaza samarwa jama’ar kasar ta tataccen mai domin amfani da shi a cikin gida, abinda ya sa ta koma sayowa daga kasashen ketare domin wadata gida.

Wannan matsala ya taimaka gaya wajen hana tattalin arzikin kasar samun habakar da ake bukata saboda yadda take kasha makudan kudade wajen sayo man.

Yanzu haka kasar na fama da karancin tatacacen man saboda korafin da dilallai suka gabatar wanda ke cewa rashin samun kudin dalar Amurka da za su sayo man na haifar musu da matsala sosai wajen shigar da tataccen man cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.