Isa ga babban shafi

Har yanzu Najeriya ta gaza kamo fursinoni 422 da suka tsere daga gidan yarin Kuje

A Najeriya wasu bayanai na nuni da cewa watanni 4 bayan harin gidan yarin Kuje da ke garin Abuja fadar gwamnati har yanzu akwai fursunonin fiye da 400 da suka tsere kuma ba tare da hukumomin kasar sun iya nasarar kamo su don dawo da su gidan yarin ba.

Fursinonin 422 suka tsere daga gidan yarin na Kuje.
Fursinonin 422 suka tsere daga gidan yarin na Kuje. © Afolabi Sotunde, Reuters
Talla

Yayin harin na gidan yarin Kuje a ranar 5 ga watan Yulin shekarar da muke cike alkaluma sun nuna cewa akwai fursinoni akalla 879 da suka tsere ciki har da gagga-gaggan masu laifi da suka kunshi ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram 64.

Alkaluman baya-bayan nan da jaridar Punch ta wallafa sun nuna cewa, har zuwa yanzu mahukuntan Najeriyar basu iya kamo fursinonin 422 ba.

Mahukuntan gidan yarin sun sanar da kamo fursinoni akalla 32 cikin 454 da suka tsere daga watan Yuni zuwa yanzu a harin wanda kungiyar ISWAP ta yi ikirarin kaiwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.