Isa ga babban shafi

Najeriya: 'Yan Bindiga na tsarewa zuwa Nasarawa - Gwamna Sule

A Najeriya, Kwana biyu bayan umarnin rufe makarantu a  jihar Nasarawa, gwamnan jihar Abdullahi Sule, ya koka kan yadda wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne dake tserewa daga Neja da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna ke kwarara zuwa Nasarawa.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust
Talla

Gwamnan ya ce bayan hango gungun ‘yan bindigan a Rugan Juli da Rugan Madaki a Karu; dake Kananan hukumomin Wamba da Toto, yasa aka fadada taron tsaro da aka gudanar a gidan gwamnati dake Lafia.

Gwamna Sule ya bayyana cewa dalilin da ya sa aka fadada taron tsaro na gaggawa shi ne daukar kwararan matakai duba da yanayin tsaro da kasar ke fuskanta, ciki harda babban birnin tarayya Abuja, inda fursunoni sama da 800 suka tsere daga gidan yarin Kuje kwanan nan.

Ya tabbatar da cewa rahotannin tsaro sun nuna cewa, biyo bayan kwararowar wadannan ‘yan bindiga da ake zargin an samu karuwar masu garkuwa da mutane a cikin watanni biyu da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.