Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kashe mutane dubu 3 da 478 cikin watanni 6 a Najeriya

Wani bincike a Najeriya ya ce akalla mutane dubu 3 da 478 aka kashe a Najeriya tsakanin watan Disambar bara zuwa Yunin bana, yayin da aka sace wasu dubu 2 da 256 sakamakon tabarbarewar tsaron da ya addabi kasar.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Kungiyar da ke sanya ido akan harkokin tsaro da ake kira ’Nigeria Security Tracker’ da ke samun goyan bayan wata Majalisa a Amurka ta gabatar da wadannan alkaluma masu tada hankali.

Rahotan kungiyar ya danganta kisan da kuma sace mutanen da akayi a cikin watanni 7 da suka gabata da ayyukan ‘Yan ta’adda da ‘Yan bindiga da ‘Yan fashi da makami da ‘Yan kungiyar asiri da kuma jami’an tsaro.

Alkaluman da kungiyar ta gabatar yace a watan Disambar bara, an kashe ‘Yan Najeriya 342, yayin da aka sace wasu 397, cikin wadanda aka kashe harda manoma 45 a Jihar Nasarawa da kuma mata 34 da aka sace a Jihar Zamfara.

A watan Janairun wannan shekara, kungiyar tace akalla mutane 844 aka kashe, yayin da aka sace 603, cikin su harda mutane sama da 200 a yankunan Jihar Zamfara da 220 da aka kasha a Neja, sai kuma 200 da aka sace a Jihar.

A watan Fabarairu kuma, kungiyar tace mutane 495, bayan sace 326, cikin su harda 33 wadanda suka ki biyan harajin naira miliyan 40 da yan bindiga suka sanya musu a Jihar Zamfara, sai kuma 44 da aka kashe a Jihar Neja, tare da sace 31.

Sakamakon binciken yace a watan Maris, mutane 606 akayi asarar rayukan su, tare da sace wasu 450 cikin su harda Yan Sakai 63 a Jihar Kebbi da kuma mutane 26 da aka kashe a harin da ake danganta shi da ramako a Jihar Taraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.