Isa ga babban shafi
Kaduna-Ta'addanci

Harin jirgin kasa: 'Yan ta'adda sun sake wata fasinja mai juna biyu

A Najeriya ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan na da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, sun sallami wata mace mai juna 2 daga cikin fasinjojin.

Jirgin kasa da 'yan ta'adda suka kai wa hari a kan hanyarsa zuwa Kaduna daga Abuja.
Jirgin kasa da 'yan ta'adda suka kai wa hari a kan hanyarsa zuwa Kaduna daga Abuja. © Daily Trust
Talla

A wani hoton bidiyo da  wata jaridar kasar ta samu, matar, wadda ba a bayyana sunata ba, ta yi kira ga gwamnatin kasar ta tattauna da ‘yan ta’addan  don ceto rayuwar wadanda suka saura a hannunsu.

Ta ce masu garkuwar sun ba su kulawa da ta dace, ta wajen ciyarwa da kula da lafiyarsau.

Jaridar ‘Daily Nigerian’ da ake wallafawa a kasar ta ruwaito wata majiya na cewa ba a biya kudi fansa a kan matar mai juna biyu ba.

Majiyar ta kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa wata mata ta haihu a sansanin ‘yan ta’addan.

gwamnatin tarayyar Najeriya ta sha alwashin kubuto fasinjoji 60 da ke hannun ‘yan ta’addan, wadanda suka shiga hannunsu a ranar 28 ga watan Maris, amma har yanzu babu wani zance mai karfi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.