Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna-'Yan Bindiga

Gumi ya kaddamar da kungiyar kare hakkin Fulani makiyaya

Shaharren malamin  addinin Musuluncin nan dake Najeriya Sheikh Ahmad Gumi ya  kafa kungiya da za ta kare hakkin Fulani makiyaya.

Shiekh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Shiekh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi YouTube
Talla

Gumi ya sanar da kafa wannan kungiya da ya kira Nomadic Rights Concern, NORIC a takaice a yayin gudanar da tafsirin watan Ramadan a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna a arewacin Najeriya.

Ya ce kungiyar za ta janyo hankali al’umma a game da cin zarafin Fulani makiyaya da ake yi.

 Ya bayyan Farfesa Umar Labbo a matsayin wanda zai jagoranci kungiyar, yana mai cewa NORIC za ta zama wata kafa da makiyaya za su kai korafe korafensu a game da abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya zuwa ga hukumomin da suka dace.

Ya kara da cewa makiyayan za su kai korafensu wajen kungiyar NORIC, wadda ita za ta taimaka musu ta wajen daukar mataki na shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.