Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe dan kasuwar kano duk da sun karbi kudin fansa

Wasu masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a Najeriya sun kashe wani dan kasuwar daga jihar Kano duk kuwa da cewa sun karbi kudin fansa daga ‘yan uwansa.

Hoton 'yan bindiga domin misali.
Hoton 'yan bindiga domin misali. © India TV News / PTI
Talla

Mutumin mai suna  Umar Sani, wanda ake wa inkiya da Magaji  ya shiga hannun ‘yan bindigar ne a makonni 2 da suka wuce a kan hanyarsa ta zuwa Buruku, amma  daga bisani aka samu tabbacin cewa  wadanda suka yi garkuwa da shi sun kashe shi bayan sun karbi kudin fansa.

Wani dan uwan mamacin, Hussaini Sani, wanda ya tabbatar da  aukuwar lamarin a ranar Juma’a, ya kuma ce sai da masu garkuwar suka sake kiransu  suna neman a basu karin Naira miliyan 20 duk kuwa da cewa sun kashe musu dan uwa.

Wannan lamari na zuwa ne kwanaki 10 bayan da iyalan wani dan kasuwa suka gano gawarsa bayan da suka biya diyyar Naira miliyan 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.