Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara

Sojin Najeriya sun kashe jagororin 'yan bindiga a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara a Najeriya sun tabbatar da kisan wasu jagororin ‘yan bindiga da jami’an tsaro suka shafe tsawon lokaci suna nemansu ruwa a jallo, wadanda suka kunshi Alhaji Auta da kuma Kachalla Ruga.

Jami'an tsaro na sintiri a jihar Zamfara ta Najeriya.
Jami'an tsaro na sintiri a jihar Zamfara ta Najeriya. © REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo
Talla

Jaridun Najeriya sun ruwaito cewa jagororin ‘yan bindigar 2 sun gamu da ajalinsu ne a wani luguden wutar sojin sama a dazukan Gusami da Tsamre na karamar hukumar Birnin Magaji da sanyin safiyar jiya asabar.

Majiyoyin Sojin sun ce yanzu haka ana laluben maboyar wasu kasurguman ‘yan bindigar da suka addabi jihar da suka kunshi Alhaji Nashama da Shingi da kuma Halilu.

Wannan nasara ta Sojin Najeriya na zuwa a dai dai lokacin da 'yansandan jihar Kaduna kuma suka yi nasarar ceto fararen hula har mutum 9 daga hannun 'yan bindiga yayin wani gumurzu tsakaninsu.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da yadda jami'an 'yan sandan suka kai sumame kan maboyar 'yan bindigar masu garkuwa da mutane da ke cikin dajin Sabon Birni a ranar 31 ga watan Disamban da ya gabata.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Kaduna ta tabbatar da yadda jami'anta suka yi nasarar tarwatsa wasu sansanoni da kuma maboyar 'yan bindigar da ke cikin dajin.

Matsalar hare-haren 'yan bindiga dai na ci gaba da samun gindin zama a jihohin arewa maso yammacin Najeriya yayinda garkuwa da mutane don neman fansa ya zama ba sabon abu ba musamman a jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina da Neja da kuma Kaduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.