Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

Kashe 'yan bindiga shi ya fi dacewa da su - El-Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna ta Najeriya Nasir El-Rufa’I ya hakikance cewa dole ne a kashe ‘yan bindigar da ke addabar al’umma domin kuwa bai amince da zancen yi musu afuwa  ko kuma gyaran halayyarsu ba.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i Twitter@GovKaduna
Talla

Gwamnan ya ce, hanya mafi dacewa wajen hulda da ‘yan bindigar da sauran ‘yan ta’adda da ke haddasa rashin tsaro a kasar, ita ce a aika su lahira.

Gwamnan ya bayyana matsayarsa ce a yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa a jiya Talata jim kadan da kammala ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari.

EL-Rufa’I ya ziyarci shugaban kasar domin yi masa bita kan hare-haren da ‘yan bindiga suka kaddamar kan jama’a a baya-bayan nan a  Kaduna, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 40.

Ba a karon farko ba kenan da gwamnan ya sha bayyana cewa, bai dace a yi sulhu da wadannan mutane masu kisan jama'a ba gaira ba dalili ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.