Isa ga babban shafi
Najeriya-Kannywood

Kannywood ta yi rashin fitaccen marubuci

Yau  aka yi janaizar Alhaji Umaru Danjuma Katsina da aka fi sani da Kasagi, daya daga cikin fitattun marubuta kuma masu shirin fina-finan Hausa a Arewacin Najeriya.

Shahararren marubucin Hausa, Umaru Danjuma Katsina (Kasagi)
Shahararren marubucin Hausa, Umaru Danjuma Katsina (Kasagi) © Mohammed Mohammed Facebook
Talla

Rahotanni sun ce Kasagi wanda ya rubuta fitaccen littafin da aka yi wa suna ‘Kulba na Barna’ ya rasu ne sakamakon gajeruwar rashin rashin lafiya.

Danjuma Katsina na daya daga cikin fitattun masu wasan kwaikwayon da suka yi suna daga shekarar 1980 tare da wasu abokan aikin sa a lokacin irin su Kasimu Yero da Tumbuleke da Malam Mamman da karkuzu Na Bodara da kuma Samanja Mazan Fama.

Kasagi ya bada gudumawa sosai wajen daga darajar wasan kwaikwayo da ake sawa a wancan lokaci a Gidan Rediyo da talabijin Kaduna, yayin da littafin sa na ‘Kulba Na Barna’ ya shiga cikin jerin litattafan adabin da suka dauke hankalin dalibai da masu sha’awar karance karance na wancan lokaci.

Rahotanni sun ce an kammala jana’izarsa a birnin Katsina wadda ta samu halartar daruruwan mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.