Gwamnati ta bukaci soke hawan Sallah a wasu jihohi saboda Korona
Gwamnatin Najeriya ta bukaci gwamnonin jihohin arewacin kasar, Sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki da su dakatar da bukukuwan hawan Sallah babba domin dakile yaduwar annobar Korona.
Wallafawa ranar:
Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin yaki da annobar Korona na Najeriya Boss Mustapha ne ya fitar da sanarwar yau Lahadi a birnin Abuja.
Matakin gwamnatin Najeriyar dai ya biyo bayan sanya jihohi shida da kuma birnin Abuja cikin matakin tsaurara matakan dakile yaduwar Korona, annobar da wasu kwararru kan sha’anin lafiya ke gargadin yiwuwar sake barkewarta a zango na 3, idan ba a dauki matakan da suka dace ba.
Jihohin da lamarin ya shafa dai sun hada da Legas, Oyo, Kano, Filato, Kaduna, Rivers da kuma birnin Abuja.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu