Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

'Yan bindiga sun saki sarkin Kajuru a jihar Kaduna ta Najeriya

Rahotanni daga jihar Kaduna a tarayyar Najeriya na cewa ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da sarkin Kajuru jihar Mai martaba Alhaji Alhassan Adamu sun sako shi da yammacin yau litinin.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i. © Twitter@GovKaduna
Talla

Wasu bayanai kamar yadda jaridun Najeriyar suka wallafa na cewa da misalin karfe 5 na yammaci ne ‘yan bindigar suka sako sarkin na Kajuru mai shekaru 85 bayan shafe kwana guda a hannun su.

Sai dai bayanan da masarautar ta fitar ta bakin kakakinta Dahiru Abubakar sun ce sun ce har zuwa yanzu ‘yan bindigar ba su sako sauran iyalan sarkin da fadawa su 13 da tun farko suka sace su a tare ba.

A safiyar yau ne dai 'yan bindigar suka bukaci biyansu fansar miliyan 200 matukar ana bukatar su saki sarkin iyalansa.

Zuwa yanzu dai babu tabbacin adadin kudin da aka biya gabanin sakin sarkin na Kajuru a jihar Kaduna.

Satar mutane don neman fansa ba sabon abu ba ne a sassan arewacin Najeriyar musamman jihohin Kaduna Katsina da Zamfara inda hare-haren 'yan bindiga ke tsananta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.