Isa ga babban shafi
Najeriya - Tsaro

'Yan bindiga sun sace Sarkin Kajuru da Iyalan sa

A Najeriya Wasu ’yan bindiga sun sace Sarkin Kajuru mai daraja ta biyu, Alhaji Alhassan Adamu a gidansa da ke Kajuru a Jihar Kaduna.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust
Talla

Jikan basaraken, kuma mai rike da sarautar Dan Kajuru a masarautar, Sa’idu Musa ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Daily Trust, Ya mai cewa da misalin karfe 12.30 na daren Asabar agogon Najeriya lamarin ya faru.

Jaridar tace, ’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da iyalan basaraken su 12, ciki har da mata da kananan yara.

Zamfara

A wani labarin kuma, ’Yan bindiga a Jihar Zamfara sun sace shugaban Kwalejin horas da aikin noma da Kimiyyar Dabbobi ta Jihar, Habibu Mainasara, a gidansa da ke garin Bakura da sanyin safiyar yau Lahadi.

Hakan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da ’yan bindigar suka hallaka kimanin manoma 40 a wansu jerin hare-hare da suka kai kauyuka biyar da ke Jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.