Isa ga babban shafi
Najeriya - Buhari

Buhari ya bada umurnin murkushe masu garkuwa da mutane

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen ƴan bindiga dake kara ta’azzara  a jihohin Zamfara da Kaduna.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. © Nigeria Presidency
Talla

A cikin wata sanarwa da mataimakinsa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya buƙaci sojojin ƙasar da su gaggauta kawo karshen matsalar a “yaren da yan bindigar za su fahimta.”

Wannan na zuwa ne bayan harin da ƴan bindiga suka kai a yankin Maradun a jihar Zamfara inda suka kashe sama da mutane 40.

Haka kuma ƴan bindiga sun kai jerin hare-hare a Kaduna inda suka sace ɗaliban makaranta a makon da ya gabata.

A cikin makon da ya gabata wasu mazauna yankin Sabon Tasha dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, sun gudanar zanga-zangar nuna bacin rai kan fargabar da ta mamaye su a dalilin fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.