Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

'Yan bindigar da suka sace daliban Nuhu Bamalli sun nemi naira miliya 22

A Najeriya, ‘yan bindigar da suka sace daliban makarantar kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli a jihar Kaduna makonni biyu da suka wuce, sun bukaci a biya su kudin fansa da ya kai naira miliyan 22 da rabi na gaba daya wadanda ke komarsu.

Hare-haren 'yan bindiga sun salwantar da rayuka da dama a arewacin Najeriya
Hare-haren 'yan bindiga sun salwantar da rayuka da dama a arewacin Najeriya Jakarta Globe
Talla

Rahotanni sun ce masu satar mutanen sun tuntubi iyalan dalibai 7 daga cikin wadanda suka sacen, da na wasu malamai 2 da ke hannunsu, inda suka nemi kudin fansar.

Wani dan uwan daya daga cikin wadanda aka sacen ya ce tun da farko barayin sun nemi a biya naira miliyan 10 a kan kowane mutum, amma daga baya suka rage kudin zuwa miliyan 2 da rabi bayan tattaunawa mai tsawo.

Ya ce tun da farko ‘yan bindigar sun yi alkawarin sakin wasu matan aure daga cikin wadanda suka sace, amma da aka bijiro musu da batun suka ce sai lokaci ya yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.