Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun sace wasu matafiya a hanyar Kaduna zuwa Kachia

Rundunar ‘yan sandan jihar kaduna a Najeriya ta ce wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kan wasu matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Kachia a jiya Juma’a, inda suka sace mutanen da ba a tantance adadinsu ba.

Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga.
Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga. Getty Images/iStockphoto - zabelin
Talla

Mai magana da yawun rundunar Mohammed Jalige ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata ganawa da ya yi da kamfanin dillancin labaran Najeriya.

Mr Jalige ya ce an samu motoci da babu kowa a cikinsu a inda lamarin ya auku, kuma an tadda wani mutum da ya samu raauni, kuma ba a yi wata wat aba wajen garzaya da shi asibiti.

Wani ganau ya ce da misalin karfe 3 na ranar Juma’a ne ‘yan bindigar suka far wa mutane a yankin Makyalli, a kan hanyar Kaduna zuwa Kachia.

A cewarsa, yana kan hanyar ce wasu suka ankarar da shi kafin ya karasa inda ‘yan bindigar suke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.