Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

Hukumar DSS ba ta gayyace ni ba - Gumi

Shahararren malamin addinin Musuluncin nan, a Najeriya,  Sheikh Ahmad Gumi, ya musanta rahotannin da ke cewa hukumar tsaro ta DSS ta gayyace shi.

Sheikh Dr. Ahmed Mahmoud Gumi a yayin ziyartar 'yan bindiga.
Sheikh Dr. Ahmed Mahmoud Gumi a yayin ziyartar 'yan bindiga. Daily Trust
Talla

Peter Afunanya, kakakin DSS ya ce hukumar ta gayyaci fitaccen malamin, inda ya ce ba wani sabon abu bane irin wannan gayyatar.

Amma a wata ganawa da ya yi da jaridar ‘Daily Trust’ a Najeriya, Sheikh Gumi ya ce ba wanda ya gayyace shi.

Gumi, ya bayyana rahoton kama shi a matsayin aikin hannun masu fatan hakan ya faru da shi.

Malamin ya ce da sanin hukuma ya ke kokarin lalubo mafita a game da matsalar tsaro da ta addabi arewacin kasar, yana mai cewa dukkannin tafiye tafiyen da ya yi cikin daji don ganawa da ‘yan bindiga, ya yi su ne tare da jami’an tsaro, hakimai , da wasu jami’an gwamnati.

ya nanata cewa babu wanda ya gayyace shi, kafafen yada labarai ne kawai ke yayata labarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.