Isa ga babban shafi
Najeriya - Neja

Jami'an tsaron Najeriya sun ceto mutane 14 daga 'yan bindiga a Neja

Hadin gwiwar jami’an ‘yan sanda, da na hukumar DSS da kuma mafarauta sun samu nasarar ceto mutane wasu 14 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su, a yankin Gauraka dake jihar Neja.

Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya.
Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya. AFP
Talla

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja Maryam Yusuf ta ce sun samu nasarar ceto mutanen 14 bayan shafe lokacin da zaratan jami’an tsaron da mafarauta suka yi suna musayar wuta tsakaninsu da ‘yan bindigar, inda suka tarwatsa sansaninsu dake yankin Byhazin-Bwari inda suka kame 2 daga cikin masu satar mutanen date da kwace makamansu ciki har da bindigogi kirar AK 47.

Matsalar hare-haren ‘yan bindiga da satar jama’a ta zama ruwan dare a wasu sassan jihar Neja, inda a watan Fabarairu ‘yan bindiga suka suka sace gwamman daliban makarantar sakandaren kimiyya ta Kagara dake karamar hukumar Rafi, wadanda aka saka bayan ‘yan kwanaki da sace su.

Baya ga Neja jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara da Sokoto ma na fuskantar matsalolin na hare-haren ‘yan binidgar masu satar jama’a da dabbobi musamman a yankunan karkara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.