Isa ga babban shafi

Hannun agogo ya koma baya a zaben Sarkin Zazzau

Gwamnatin Jihar Kaduna da ke Najeriya ta ce masu zaben Sarkin Zazzau sun fara wani sabon zama domin sake zaben wanda zai maye gurbin marigayi Alhaji Shehu Idris da Allah Ya yi wa rasuwa makwanni kusan biyu da suka gabata a matsayin Sarkin Zazzau na 19.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Sakataren Gwamnatin Jihar Balarabe Abbas Lawal ya sanar da haka, inda yake cewa gwamnati ta bukaci sake zaben ne saboda yadda rahotan zaben farko ya kai ga jama’a ba tare da tantancewa ba, abin da ya sa gwamnati ta soke shi baki daya.

Sanarwar ta kuma ce kafin gudanar da wancan zabe, an hana Bunun Zazzau damar gabatar da takardun takararsa, abin da ya sa ya gabatar da korafi akan zaben, tare da Sarkin Dajin Zazzau.

Gwamnatin ta ce bincikenta ya gano cewar masu Zaben Sarkin sun tantance 'yan takara biyu ne kacal a ranar 24 ga watan Satumba ba tare da duba takardun tarihin rayuwarsu ba wanda suka karba kwana guda bayan ganawa da su.

Sakataren ya ce gwamnatin Jihar Kaduna ta nuna damuwa kan yadda rahotan tantancewar ya kai ga jama’a kafin gwamnan jihar Kaduna ta samu.

Lawal ya ce yanzu haka masu Zaben Sarkin na gudanar da taro domin tantance ‘yan takara 13 da suke bukatar zama Sarkin Zazzau na 19 daga daukacin gidajen sarautar Zazzau, cikinsu har da mutanen biyu da aka hana takara a baya.

Sanarwar gwamnatin da Muyiwa Adekeye ya sanya wa hannu ta ce, da zaran an kammala, za a mika wa gwamna Nasir El-Rufai domin tantancewa da yanke hukunci a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.