Isa ga babban shafi
Najeriya

Kaduna ta kori Almajirai dubu 35

Gwamnatin Jihar Kaduna ta Najeriya ta kori yara Almajirai dubu 35 zuwa jihohi 17 da suka hada da kasashe makwabta.

Jihohin Arewacin Najeriya sun kori Almajirai saboda fargabar cutar coronavirus
Jihohin Arewacin Najeriya sun kori Almajirai saboda fargabar cutar coronavirus PM News
Talla

Kwamishiniyar Jin-kadai da Inganta Rayuwar Al’umma ta Jihar, Hajiya Hafsat Baba ta sanar da haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a birnin Kaduna, yayin da ta ce, jihar ta kuma karbi sama da Almajirai dubu 1 daga wasu jihohin daban.

Kwamishiniyar ta ce, wannan matakin da aka dauka, na cikin yunkurin gwamnatin jihar na tabbatar da cewa, dukkanin kananan yara sun samu ilimin Al-Kur’ani da na zamani karkashin kulawar iyayensu.

Hajiya Hafsat ta ce, Ma’aikatarta tare da agajin Asusun Tallafa wa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNIECF, na kula da Almajiran da wasu jihohin suka taso keyarsu zuwa Kaduna.

Kwamishiniyar ta ce, wasu daga cikin Almajiran na fama da wasu nau’ukan cutuka da ke bukatar kulawa kafin sake sada su da dangoginsu.

Bullar abbobar coronavirus ce ta tilasta wa gwamnatocin johohin arewacin Najeriya mayar da dubban Almajirai jihohinsu na asali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.