Isa ga babban shafi
Duniya-Coronavirus

Yadda Musulmi suka yi Sallah a sassan duniya karkashin matakan dakile corona

Yau mafi akasarin al’ummar Musulmi a sassan duniya da suka hada kasashen Asiya, Gabas ta Tsakiya ciki harda yankin Falasdinu, Turai da ma kasashen Afrika ke bikin Sallar Idi karama bayan cika kwanaki 30 na watan Azumin Ramadana.

Al'ummar Musulmi yayin Sallar Idi a Bangkok, babban birnin Thailand.
Al'ummar Musulmi yayin Sallar Idi a Bangkok, babban birnin Thailand. Reuters
Talla

Bikin Sallar karama ta bana ta zo ne cikin yanayi na matakan killace jama’a da kuma takaita zirga-zirga gami da hana taron jama’a saboda dakile yaduwar annobar coronavirus.

Rahotanni sun ce duk da matakan takaita taron jama’ar, a wasu daidaikun yankunan kasashe, al’ummar Musulmin a yau sun samu damar halartar Sallar Idi bayanda hukumominsu suka yanke shawarar sassauta dokokin killacewar da a baya suka kafa saboda cutar ta coronavirus, inda Ibadar ta gudana bisa tsarin bada tazara saboda neman kariya daga cutar.

Sai dai Sallar Idin karama ta bana ta sha bambam da yadda aka saba gani a shekarun da suka gabata, la’akari da yadda annobar ta tsayar da sufuri a fadin duniya, yanayin da ya hana mutane tafiye-tafiye don ziyartar ‘yan uwa da abokan arziki a ciki da wajen kasashen da suke.

A mafi akasarin kasashen da al’ummar Musulmi suka fi rinjaye kamar su Turkiya, Qatar, da Indonesia hukumomi sun soke gudanar hada-hadar karamar Sallah kamar yadda aka saba, ciki harda Sallar Idi.

A Saudiyya, Masallatai an yi amfani da kafafen sadarwa wajen isar da kiran Sallar Idi, sai dai ba baiwa mutane damar halartar Masallatan Harami ba, irin matakin da aka dauka a watan Azumin Ramadana.

A nahiyoyin Arewaci da kuma Kudancin Amurka kuwa inda al’ummar Musulmi basu da rinjaye, bikin Sallar karama na gudana ne a karkashin dokokin takaita zirga-zirga da taron jama’a saboda annobar COVID-19.

Wani batu da ya dauki a hankula a bana dai shi ne yadda kungiyoyin Musulmi, Malamai da sauran daidaiku suke amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen isar da sakwanni da kasidu kan koyarwar addinin Musulunci.

Dangane da yadda bikin Sallar karama ya gudana a sassan duniya sashin Hausa na RFI ya leka wasu kasashe inda ya tattauna da mutane daban daban cikin shirin da Ahmad ya jagoranta.

20:17

Yadda Musulmi a sassan duniya suka yi Sallah karama karkashin matakan dakile corona

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.