Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya nemi a binciki cinikin makamai a Najeriya tun daga shekarar 2007

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci mai bashi shawara kan harkokin tsaro, ya kafa kwamitin da zai bincikin yadda aka yi cinikin makamai da alburusai, da aka sayo wa dakarun kasar, tun daga shekarar 2007 zuwa yanzu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari opinionnigeria.com
Talla

Wata sanarwar da mai baiwa shugaban shawara na musamman, kan harkokin yada labaru Femi Adesina ya fitarm tace gwammnatin na so ta gano irin muna munar da aka yi a bangaren, tare da bayar da shawar kan yadda za a kaucewa hakan nan gaba.
Sanarwar ta bayyana membobon kwatin kamar haka;
AVM J.O.N. Ode (Mai Murabus) – Shugaba
R/Adm J.A. Aikhomu (Mai Murabus) – Mamba
R/Adm E. Ogbor (Mai Murabus) – Mamba
Brig Gen L. Adekagun (Mai Murabus) – Mamba
Brig Gen M. Aminu-Kano (Mai Murabus) – Mamba
Brig Gen N. Rimtip (Mai Murabus) – Mamba
Cdre T.D. Ikoli – Mamba
Air Cdre U. Mohammed (Mai Murabus) – Mamba
Air Cdre I. Shafi’i – Mamba
Col A.A. Ariyibi – Mamba
Gp Capt C.A. Oriaku (Mai Murabus) – Mamba
Mr. Ibrahim Magu (EFCC) – Mamba
Brig Gen Y.I. Shalangwa – Sakatare
Sanarwar ta kara da cewa, kafa kwamitin ya biyo bayan kalu balen da dakarun kasar suka yi ta fuskanta ne, a kokarin da suke yaki da ayyukan ta’addanci a arewa maso gabashin kasar, sakamakon rashin kayan aiki, lamarin da yasa basu da kwarin gwiwar gudanar da ayyukansu.
Kwatin zai binciki yadda aka gagara bin hanyoyin da suka dace, wajen samar da kayan aikin ga sojojin, tare kuma da rashin aiki da sassan da suka dace, daga rundunonin kasar wajen sayen makaman.
Wadannan matsalolin, a cewar sanarwar, sun taimaka wajen sayen makamai marasa inganci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.