Sojojin Najeriya sun kashe 'Yan Boko Haram a Borno
A Najeriya, Sojoji sun yi nasarar hallaka wasu mutane 10 da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne bayan sun kai farmaki kan ayarin motocin da babban hafsan sojin kasar, Laftanal Janar Tukur Buratai ke ciki.
Wallafawa ranar:
Al-amarin dai ya haifar da musayar wuta tsakanin sojojin da mayakan kamar yadda majiyar sojin ta sanar a yau lahadi.
Majiyar ta bayyana cewa, Jami’in Soji daya ne ya rasa ransa, kuma babu abinda ya samu Buratai wanda ya shirya kai ziyara ga rundunar dake Arewa maso gabashin Kasar yayin da ‘yan bindigan suka kaiwa tawagar sa hari a kauyen Faljari mai nisan kilomita 45 daga birin Maiduguri na jihar Borno.
A bangare guda, sojojin sun kama mutane 5 daga cikin yan bindigan kuma Sojoji biyar sun samu raunuka a fafatawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu