Isa ga babban shafi
Najeriya

Jam'iayyar APC ta bayyana sabbin manufofinta ga 'yan Najeria

Jamiyar APC a Najeriya ta bayyana manufofi uku da gowanatin ta zata fi bawa fifiko in ta karbi ragamar mulki a ranar ashirin da tara na wannan wata na mayu. Jamiyar ta bayyana hakane a wani taro da ta gudanar a birnin Abuja, inda tayi da nazarin manufofin da tsare tsaren gwamnati mai shigowa karkashin jagorancin Shugaba mai jiran Gado Muhammadu Buhari.Jam’iyyar tace gwamnatin zata mayar da hankali ne wajen samar da tsaro, aikin yi ga matasa da kuma yaki da cin hanci da rashawa.Sai dai kuma akwai wadanda suke ganin samar da wadannan abubuwan suna da wuya ga sabuwar gwamnatin a halin da ake ciki. 

Zababben shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Zababben shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari AFP PHOTO /STRINGER
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.