Isa ga babban shafi
MDD-Najeriya

Idan an saki 'Yan matan Chibok zasu samu tallafi

Majalisar Dinkin Duniya tace zata taimakawa Najeriya ceto daliban Makarantar Sakandare da Mayakan Boko Haram Suka sace a Chibok tare da yin alkawalin ba 'Yan matan da iyayensu da al'ummar Chibok tallafi da zarar an kubutar da su.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon REUTERS/Shannon Stapleton
Talla

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman, Said Djinit ne ya bayyana haka a birnin Abuja bayan kammala ziyarar kwanaki hudu a kasar, inda ya gana da hukumomin kasar a fannoni dabam dabam.

Jakadan ya shaidawa manema labarai cewa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin duniya Ban Ki-moon yana goyan bayan gwamnati da mutanen Najeriya, a cikin wannan hali da suka samu kansu, tare da yin Allah wadai da sace daliban.

Jakadan ya bayyana shirin Majalisar na bayar da tallafi na musamman ga iyalan daliban da mutanen Chibok da kuma 'yan matan da zaran an sako su, ta hanyar ba su kula wadda zata taimaka musu komawa cikin al'umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.