Isa ga babban shafi

Iran ta inganta makamashin nukiliyarta zuwa kashi 60

Iran ta fara tace makamashin Uranium zuwa ingancin kashi 60 a tashar nukiliyarta ta Fordo, wadda aka sake budewa a shekarar 2019 a daidai lakacin da aka gaza ceto yarjejeniyar nukiliyarta da manyan kasashen duniya, kamar yadda rahotanni suka nuna a yau Talata.

Shugaban Iran Ebrahim Raisi.
Shugaban Iran Ebrahim Raisi. AP
Talla

Kamfanin Dillancin Labaran Iran  na ISNA ya tabbatar da wannan labari, inda ya rawaito cewa a karon farko kenan,  kasar ke tace makamashin Uranium zuwa kashi 60.

Ana dai bukatar ingancin Uranium ya kai kashi 90 ne kafin samar da makamin kare dangi, saboda haka kashi 60 da Iran ta tace, na nufin cewa, ta kama hanyar cimma wannan  shu’umin makamin.

Iran ta sha musanta cewa tana da kudirin samar wa kanta makamin kare dangi na nukiliya, inda ta dage kan cewa,  tana inganta makamashin Uranium din ne domin samar da abubuwan more rayuwa ga al’ummarta.

A karkashin yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015, Iran ta amince ta takaita ayyukan da take yi a tashar nukliyar Fordo, inda za ta rika tace makamashin Uranium zuwa ingancin kashi 3.67, wanda hakan ma ya isa ya amfanar da fararen hularta.

Hakan ne ma ya sa manyan kasashen duniya suka amince su sassauta wa Iran din takunkuman karayar tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.