Isa ga babban shafi

Gazawar shugabanni ta tilasta jama'a juya baya ga mulkin demokradiyya- Bincike

Wani sabon rahoto da cibiyar nazarin demokradiyya da tsarin tafiyar da zabe ta kasa da kasa da ake kira IDEA ta fitar ya nuna yadda al’umma fara juya baya ga mulkin Demokradiyya inda suke fifita jagorancin shugabannin da ba na Demokradiyya ba, sakamakon gazawar tsarin na demokradiyya a wasu kasashe.

Demokradiyya na ci gaba da samun koma baya ne sakamakon gazawar shugabanni kamar yadda masana ke ikirari.
Demokradiyya na ci gaba da samun koma baya ne sakamakon gazawar shugabanni kamar yadda masana ke ikirari. AFP - RAJESH JANTILAL
Talla

Wani bincike da cibiryar ta IDEA ta gudanar ya nuna yadda masu kada kuri’a a kasashe 19 da suka kunshi 3 mafiya karfin demokradiyya a duniya da kuma wasu 3 daga nahiyar Afrika sun bayyana cewa zabinsu a siyasance bai da muhimmanci, maimakon haka zasu fi son jagorancin jajirtaccen shugaban da ba na demokradiyya ko kuma wanda ba zababbe ba.

Rahoton wanda IDEA ta fitar a yau Alhamis ta ce galibin wadanda ke goyon bayan jagorancin shugabannin da ba na demokradiyya ba na da nasaba da yadda zababbun shugabannin da suka marawa baya suka gaza cimma muradan da al’umma suka zabesu dominsu.

Cibiyar ta IDEA mai mambobi 35 da ke da shalkwata a Sweden wadda kuma ke rajin bunkasa demokradiyya a kasashen duniya ta ce yanayin yadda tunanin rukunin farko na mutane ke sauyawa game da demokradiyya manuniya ce ga yadda tsarin ke sanyaya gwiwar wadanda suka yi amanna da shi.

Rahoton ya ce rukuni na biyu na mutanen da ta gudanar da bincike kansu a kasashe 19 da suka kunshi mata da kuma kabilun tsiraru sun nuna shakka kan yiwuwar demokradiyya ta yi tasiri wajen tabbatar da sahihin shugabanci.

IDEA ta gudanar da wannan bincike a kasashen Brazil, da Chile da Colombia kana Denmark da Gambia da India sannan Iraq da Italiya.

Sauran kasashen da wannan bincike ya gudana sun kunshi Lebanon da Lithuania da kuma Pakistan sannan Romania da Senegal da Saliyo tsibirin Solomon sannan Korea ta kudu da Taiwan da Tanzania da kuma Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.