Isa ga babban shafi

Filin jirgin Sama na birnin Madrid ya cika makil da bakin haure da ke neman mafaka

Filin jirgin saman Madrid na fama da kwararar masu neman mafaka dake shiga birnin daga Afirka da ba a taba ganin irinsa ba, wadanda ke kwana a cunkushe kuma cikin datti, lamarin wanda hakan ya sa kungiyar agaji ta Red Cross ta daina gudanar da wata hidima a can don nuna adawa da hakan.

Wasu daga bakin haure da ke neman mafaka a Turai
Wasu daga bakin haure da ke neman mafaka a Turai REUTERS/Guglielmo Mangiapane
Talla

 

Daruruwan bakin haure, wadanda akasari daga kasar Senegal suke zuwa kasar, a makonnin baya-bayan nan suka nemi mafaka bayan da suka shiga birnin na Madrid a lokacin da suke jinkirin zuwa wasu kasashe, galibinsu a Kudancin Amurka wadanda suke samun nasarar ba tare da wata bukata ta biza ba.

Yayin da suke jiran a samun izini an ajiye su a dakunan da aka tanadar da dakunan wanka da aka kebe domin bakin haure da ke neman mafaka.

Gwamnati ta bude daki na hudu don tinkarar matsalar yawan bakin hauren amma har yanzu ana tilastawa wasu masu neman mafaka kwana a kan katifu masu hura wuta ko kuma mutum biyu su kwana a katifa guda, a cewar Hukumar agazawa 'Yan Gudun Hijira ta Spain (CEAR), mai zaman kanta.

“Matsalar cunkoson jama’a da rashin tsafta ya tsananta a wannan wuri, lamarin da ya haifar da fuskantar matsalar kudin cizo, da tarin shara da kuma karancin tawul don tsaftace jikin mutum,” in ji sanarwar da hukumar ta fitar.

Bidiyon da jami'an 'yan sandan filin jirgin suka aika wa kafofin yada labarai sun nuna tarin kyankyasai a wurin saboda rashin tsafta.

Adadin bakin haure da aka samu a filin jirgin saman Madrid a karshen watan Janairu ya kai tsakanin dari 390 zuwa 450, a cewar hukumar ta CEAR da kungiyar 'yan sanda SUP, daga 250 a karshen watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.