Isa ga babban shafi

An samu raguwar masu busa taba sigari a duniya cikin 2023- WHO

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta sanar da samun raguwar masu busa taba sigari a sassan Duniya duk da cewa har zuwa yanzu akwai mutane biliyan 1 da miliyan 250 da ke shan sigari, dai dai lokacin da kiraye-kiraye da kuma gargadin masana ke ci gaba da karuwa kan illar zukar sigarin ga lafiyar bil’adama.

WHO ta ce kamfanonin na karkata akalarsu wajen samar da wasu nau'ikan sigari da ke da jan hankali matuka.
WHO ta ce kamfanonin na karkata akalarsu wajen samar da wasu nau'ikan sigari da ke da jan hankali matuka. AP - Tony Dejak
Talla

Wasu alkaluma da ke kunshe cikin rahoton da WHO ta fitar a yau Talata, hukumar ta ce daga bara zuwa bana alkaluman masu busa taba sigarin ya koma mutum 1 cikin 5 sabanin 1 cikin 3 a shekarar 2000.

Rahoton na WHO ya ce kasashe 50 sun yi gagarumar nasara a yakinsu da shan taba sigari, musamman kasashen Brazil da Netherlands wadanda suka gabatar da shirin MPOWER da ya tsaurarawa masu sha da fataucin sigarin, ta yadda Brazil ta rage adadin masu wannan dabi'a da kashi 35 yayinda Netherlands ta tasamma kashi 30 zuwa yanzu.

Acewar Ruediger Krech daraktan sashen lafiya na WHO a baya-bayan nan duniya na ganin gagarumar nasara a yaki da matsalar ta shan taba sigari, sai dai akwai bukatar kasashe su mike tsaye wajen kalubalantar kamfanonin da ke sarrafa taba sigarin wadanda ke karkata akalarsu zuwa samar da wasu nau’ikan sigarin masu jan hankali ga matasa wadanda ke da matukar cutarwa ga bil’adama.

Yankin kudu maso gabashin Asiya ke matsayin kan gaba wajen yawan masu ta’ammali da sigari da kashi 26.5 yayinda Turai ke da kashi 25.3.

Har yanzu kasashen Afrika ke baya a sahun yankunan da matsalar ta zukar taba sigari ta tsananta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.