COP28-An tara kudade don yaki da cututtukan da suka shafi sauyin yanayi
Taron sauyin yanayi na COP 28 da ke gudana a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, ya samar da dalar Amurka miliyan 777 domin yaki da wasu cututtuka da ka iya tsananta, a daidai lokacin da dumamar yanayi ke tsananta.
Wallafawa ranar:
A cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban taron na COP 28, Sultan Ahmed Al-Jaber ya ce, abubuwan da suka ta’allaka da sauyin yanayi sun zama wata gagarumar barazana da lafiyar bil’adama a karni na 21.
Daga cikin wadanda suka yi alkawarin bayar da kudaden yaki da cututtukan da ake addabar wasu yankuna, har da Daular Larabawa wadda ta bada dala miliyan 100 da kuma Gidauniyar Bill and Melinda Gates da ita mata bada dala miliyan 100.
Sauran kasashen sun hada da Jamus da Belgium da kuma Hukumar Raya Kasashe Masu Tasowa ta Amurka.
Wannan na zuwa ne bayan Bankin Duniya ya kaddamar da wani shiri na neman tallafin kula da bangaren kiwon lafiyar al’umma a kasashe masu tasowa, inda matsalar sauyin yanayi ke barazana wajen ta’azzara cututtaka.
Ana fargabar cututtakan ka iya tsananta saboda dumamar yanayin, kari kan barazanar da sauyin yanayin ke yi wa matsalar tamowa da malária da amai da gudawa da kuma matsancin zafi.
Ana dai iya magance cututtukan da ke addabar wani yanki cikin sauki kamar makantar rafi da kuma cutar yawan barci da ke yaduwa a nahiyar Afrika kuma ana fargabar wadannan cututtukan ka iya tsananta saboda dumamar yanayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu