Isa ga babban shafi

A karon farko hukumar lafiya ta duniya na gudanar da taro kan maganin gargajiya

A karon farko hukumar lafiya ta duniya WHO ta fara gudanar da taro kan maganin gargajiya, inda ta ce tana kokarin tattara bayanai ne domin bada damar yin amfani da maganin ba tare da ya illatar da mutane ba. 

WHO na gudanar da taro kan maganin gargajiya.
WHO na gudanar da taro kan maganin gargajiya. AFP/Stefan Heunis
Talla

Taron na kwanaki biyu, na gudana ne lokaci guda da taron ministocin lafiyar kasashen G20 a birnin Gandhinagar na kasar India.

A jawabin shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a wajen bude taron, ya ce taron zai taimaka wajen tattara alkaluma da hujjojin da suka kamata, wadanda za su baiwa hukumar damar amincewa don yin amfani da maganin gargajiya.

Shugaban majalisar kimiya ta hukumar Harold Varmus, ya shaida wa taron cewar dole ne suyi duba kan lamarin, musamman yadda a yanzu ake amfani da magungunan gargajiya, don gano masu inganci a cikinsu.

Duk da yadda ake amfani da maganin gargajiya a sassa da dama na duniya, amma kuma maganin na fuskantar suka daga bangarori daban-daban, musamman na rashin samar da hukumomin da za su rinka sanya wa bangaren ido.

Daga cikin kasashe 194 da ke karkashin hukumar ta WHO, kasashe 170 sun amince da amfani da maganin gargajiya tun a shekarar 2018, amma sai dai kasashe 124 ne kadai suka samar da dokokin amfani da maganin a kasashensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.