Isa ga babban shafi

An samar wa Afrika allurai miliyan 18 na rigakafin Malaria

Kasashen Afrika 12 za su samu tagomashin allurar rigakafin zazzabin Malaria miliyan 18 tsakanin shekarar da muke ciki ta 2023 zuwa badi 2025, kodayake Najeriya ba ta sahun kasashen da za su mori wannan tagomashi duk da kasancewarta jagora a sahun masu fama da wannan cuta da sauro ke yadawa. 

Za a dauki tsawon shekaru biyu ana rarraba alluran rigakafin Malaria a kasashen Afrika.
Za a dauki tsawon shekaru biyu ana rarraba alluran rigakafin Malaria a kasashen Afrika. AFP - BRIAN ONGORO
Talla

 

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce kasashen da za a rarraba wa alluran miliyan 18 sun kunshi Benin da Ghana da Kenya da Malawi da Burkina Faso da Kamaru da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo sai Nijar da Saliyo da Uganda da Liberia da kuma Burundi.  

Wata sanarwar hadaka tsakanin WHO da UNICEF da kuma shirin Gavi da ke samar da alluran rigakafi ta ce za a shafe shekaru 2 ana rarraba alluran rigakafin Malariyar ta RTS, S/AS01 tsakanin kasashen 12 kodayake sai a watanni ukun karshen shekara ne shirin zai kankama. 

Sanarwar hadakar ta ce anyi duba ga yankin da ya fi tsananin bukatar alluran rigakafin na RTS wato yankunan da cutar ta Malaria ke kisan kananan yara ba kakkautawa. 

Tun bayan da kasashen Ghana da Kenya da kuma Malawi suka amince da gwajin alluran rigakafin kan yara miliyan 1 da dubu dari 7 a shekarar 2019 WHO da Gavi da ya zuba kudaden samar da allurer suka tabbatar da sahihancin rigakafin kuma tun daga wancan lokaci aka sahale ci gaba da amfani da shi wanda ya taimaka wajen raguwar asarar rayukan da ake gani shekara bayan shekara a yankunan. 

Yanzu haka dai kasashen Afrika 28 suka mika bukatar karbar rigakafin cutar ta Malaria mai lakabin RTS,S/AS01 don kakkabe barazanar cutar wadda ke matsayin babbar hanyar kisa a nahiyar ta Afrika. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.